
Wannan course ɗin yana koyar da muhimman abubuwan Fiqhu na ibada kamar tsarkakewa, sallah, zakka, azumi da sauran su, cikin sauƙi da fahimta. An tsara shi ne domin kowa ya iya koyon yadda ake gudanar da ibada daidai.
Instructor
Yusuf Muhammad Umar

Premium
Included with any iHarande subscription.
Wannan course ɗin Fiqhu da Ibada a Aikace (فقه العبادات) an tsara shi ne domin koyar da Musulmai yadda ake gudanar da ibadunsu bisa ingantacciyar hanya kamar yadda shari’a ta tanada.
A cikin wannan course, za a fara da bayani kan tsarkakewa (Taharah), nau’o’in ruwa, najasa da yadda ake tsarkake kai. Daga nan za a shiga alwala, wankan janaba, tayammama, da kuma hukunce-hukuncen haila da jinin haihuwa.
Haka kuma course ɗin ya ƙunshi cikakken bayani kan sallah – daga sharuɗɗa, rukunnai, wajibbai, lokuta, sallar jam’i, Juma’a, nafila, har zuwa sujudin mantuwa, sallar matafiyi da ta mara lafiya, da kuma jana’iza.
Bayan haka, za a koyi muhimman ibadu kamar zakka da dukkan hukunce-hukuncenta, azumi da dukkan sharudda, abubuwan da ke karya shi, da kaffara.
11 lessons · 3 min
Yusuf Muhammad Umar
Instructor at iHarande.